Odisha jiha ce, da ke a Arewa maso Gabashin ƙasar Indiya. Tana kuma da yawan fili kimanin kilomita arabba’i 155,707 da yawan jama’a 45,989,232 (in ji ƙidayar shekarar 2011). Jihar tarayyar Indiya ce daga shekara ta 1936. Babban birnin jihar da birnin mafi girman jihar Bhubaneswar ne. Ganeshi Lal shi ne gwamnan jihar. Jihar Odisha tana da iyaka da jihohin huɗu: Bengal ta Yamma da Jharkhand a Arewa, Chhattisgarh a Yamma da Andhra Pradesh a Kudu.