Damaturu
Damaturu | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | Jihar Yobe | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 88,014 lissafi | ||||
• Yawan mutane | 37.2 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 2,366 km² | ||||
Altitude (en) | 371 m | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Damaturu karamar hukuma ce kuma babban birnin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.[1] Nan ne hedikwata inda fadar gwamnatin Jihar Yobe take wadda gwamna Mai Mala Buni ke mulkinta a halin yanzu, sannan kuma cibiyar gudanar da mulki na jahar. Masarautar Damaturu, ita ce masarautar gargajiya daya jal ta sarkin yanka mai daraja ta daya a gabadaya fadin birnin. Kebantacciyar lambar akwatin waya na birnin ita ce 620. Karamar hukumar tana da fadin kasa 2,366 2 da yawan jama'a 88,014 a kidayar shekara ta 2006. Garin Damaturu yana kan babbar hanyar A3. A alkaluman ilimin zanen kasa, birnin Damaturu ya gindayu ne akan alkaluman kwa'odineto 12°00′00″N 12°00′00″E / 12.00000°N 12.00000°E.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Damaturu ta kasance a matsayin mallaka a lokacin da turawan Ingila suka sassaka ta daga gundumar Alagarno . Hakan ya haifar da mamaye daular Bornu a shekara ta 1902 da sojojin mulkin mallaka karkashin jagorancin Kanar Thomas Morland suka yi.
Boko Haram
[gyara sashe | gyara masomin]Damaturu dai ya sha fuskantar hare-haren mayakan jihadi na Boko Haram a yakin da suke yi na kafa daular halifanci a yankin arewa maso gabas.
- A watan Nuwamba 2011, sun kashe sama da mutane 100 a wasu hare-hare .
- A watan Disambar 2011, sun kai hare-haren bama-bamai biyu .
- A watan Yunin 2012, mahara 40 sun shiga gidan yari . Fursunoni 40 ne suka tsere sannan aka kashe mutane takwas.
- A watan Yunin shekarar 2013 ne mahara suka kai hari wata makaranta inda suka kashe mutane goma sha uku da suka hada da dalibai da malamai.
- A watan Oktoban shekarar 2013, mayakan sun yi artabu da jami’an tsaro tsawon lokaci tare da kai farmaki a wani asibiti.
- A watan Disambar 2014, mayakan sun sake kai hare-hare. An ji karar harbe-harbe da fashe-fashe, an kuma ce an kona sansanin 'yan sandan kwantar da tarzoma. Jami'ar jihar Yobe ma an kai hari.
- A watan Fabrairun 2015, wata matashiya 'yar kunar bakin wake ta kashe mutane 16 a wata tashar mota .
- A watan Fabrairun 2020, an yi kisan kiyashi a Auno da ke kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri . Maharan sun kashe matafiya 30, sun kona motoci tare da yin garkuwa da mutane.
Yanayi
[gyara sashe | gyara masomin]Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]11°44′40″N 11°57′40″E / 11.74444°N 11.96111°EPage Module:Coordinates/styles.css has no content.11°44′40″N 11°57′40″E / 11.74444°N 11.96111°ESamfuri:Yobe State