Dapo Abiodun
Dapo Abiodun | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 2019 - ← Ibikunle Oyelaja Amosun | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Dapo Abiodun | ||
Haihuwa | Iperu (en) , 29 Mayu 1960 (64 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Bamidele Abiodun | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Obafemi Awolowo Christ's School Ado Ekiti (en) | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan kasuwa da ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Adedapo Oluseun Abiodun (an haife shi a ranar 29 ga watan Mayu shekara ta 1960) ɗan kasuwan Najeriya ne kuma ɗan siyasa, wanda ya kasance gwamnan jihar Ogun tun bayan lashe zaɓen 2019 a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressive Congress. Dapo Abiodun shi ne shugaban hukumar kula da harkokin kamfanoni. Kafin hawansa mulki, yakkasance manajan darakta na kamfanin mai na Heyden Petroleum kuma ya kafa kamfanin First Power Limited. A ranar 10 ga Maris, 2019, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta ayyana shi a matsayin Gwamnan Jihar Ogun.[1]
Haihuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Abiodun a ranar 29 ga Mayu 1960 a Iperu Remo, Jihar Ogun, ga dangin sarauta na Iperu. An haife shi a gidan Dr. Emmanuel Abiodun da Mrs. Victoria Abiodun daga Iperu Remo, a gundumar Ogun ta Gabas.[2]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Har yanzu ba a san tarihin ilimin Abiodun ba. Ya shiga cikin badakalar satifiket wajen tunkarar zaben 2015 lokacin days fito takarar sanata ya yi ikirarin cewa ya kammala karatunsa a jami’ar Obafemi Awolowo, amma a takarar gwamna a 2019 ya yi ikirarin cewa ya mallaki shaidar kammala makarantar sakandare ne kawai.
A wata hira da Seun Okinbaloye a tashoshi talabijin a watan Disamba 2018, Abiodun "Da'awar cewa bai taba samun digiri daga Obafemi Awolowo University". Ya yi ikirarin cewa shi dalibin makarantar ne amma bai kammala karatunsa a makarantar ba
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne Manajan Darakta/Shugaba na Kamfanin Mai da Gas na Najeriya Heyden Petroleum Ltd (HPL). Har ila yau rahotanni sun ce shi ne ya kafa kamfanin First Power Limited.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Abiodun da dan jam’iyyar PDP ne a jihar Ogun, duk da cewa a halin yanzu dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya sauya sheka bayan zaben 2015. Ya tsaya takarar Sanatan yankin Ogun ta Gabas a karkashin jam’iyyar APC a zaben shekarar 2015 da ya gabata a Najeriya inda ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). An zabe shi dan majalisar dattawan tarayyar Najeriya a karkashin rusasshiyar jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a shekarar 1998. Ya taba zama memba na kwamitocin shugaban kasa da kungiyoyi daban-daban. [3]
A 2019, ya tsaya takarar gwamna a jihar Ogun, ya kuma yi nasara, a karkashin jam’iyyar APC.
An rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Ogun a ranar 29 ga Mayu 2019. Shi Kirista ne kuma yana yin ibada a cocin mountain of fire and miracle ministry. Ya shaida cewa duk da adawar da aka yi masa na shiga ofishin gwamnan jihar Ogun saida Allah yabashi nasara.
Rigingimu
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2018, jaridar Cable ta yi zargin cewa Abiodun na da hannu wajen yin jabun satifiket.[1]
Sakamakon leken asirin Pandora Papers, Premium Times ta ruwaito yadda Abiodun ya shiga cikin wasu kamfanoni biyu na teku da aka fi sani da wurin biyan haraji, British Virgin Islands . Rahoton ya bayyana cewa Abiodun ya mallaki kuma shi ne darakta daya tilo na kamfanin Marlowes Trading Corporation da Heyden Petroleum Limited wanda hakan ya saba wa ka’idar da’ar ma’aikata da kuma dokar kotun shari’a kasancewar babu wani kamfani da aka bayyana a lokacin da aka zabi Abiodun a matsayin Gwamna. Shi kansa Abiodun ya kaucewa tambayoyi kan batun amma wani na hannun daman Abiodun ya yi ikirarin cewa gwamnan ya yi niyyar rusa kamfanonin ne amma bai lura ba har yanzu ba a rushe su ba.
A watan Maris na 2022 ne SaharaReporters ta buga tarihin yadda aka daure Abiodun a gidan yari a 1986 bisa laifin zamba a Miami Dade Florida, Amurka.
An ce gwamnan ya yi amfani da wani sunan bogi (Shawn Michael Davids) da nufin boye laifinsa.
Rahoton ya nuna cewa an daure Abiodun ne bisa laifin aikata laifukan da suka hada da zamba da katin kiredit, kananan sata da kuma na jabu.
An kama shi a ranar 7 ga Nuwamba, 1986, saboda fada da raunata wani dan sanda a kokarin da ya yi don kar a kama shi.
Yayin da ake tanyance shi a tasha, an binciki hoton yatsansa a cikin ma’adanar laifuka kuma an gano cewa Adedapo Oluseun Abiodun da Shawn Michael Davids Duk mutum daya me.
Ta haka ne aka tabbatar da laifinsa da tarihinsa kuma aka daure shi.
Wasu takardu da SaharaReporters ta samu sun nuna cewa, lambar gidan yari Abiodun itace 8600B943
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Yana auren Bamidele