Luca Pacioli
Luca Bartolomeo de Pacioli (wani lokaci Paccioli ko Paciolo ; c. (1447 – 19 Yuni 1517) masanin lissafin Italiya ne, Franciscan friar, ya haɗa gwiwa tare da Leonardo da Vinci, kuma shine farkon wanda ya fara bada gudummawa a fannin lissafin kuɗi. Ana yi masa lakabi da mahaifin lissafin kudi (father of accounting) kuma shi ne mutum na farko da ya fara fito da tsarin double entry system of book-keeping a nahiyar. [lower-alpha 1] Ana kuma masa lakabi da Luca di Borgo, sunan garin su inda aka haifeshi Borgo Sansepolcro, Tuscany .
Yawancin ayyukansa anyi musu hankakankanci daga Piero della Francesca, a cikin abin da ake kira "watakila farkon matsalan hankakankanci (plagiarism) a cikin tarihin lissafi". [1]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Luca Pacioli a tsakanin 1446 zuwa 1448 a garin Tuscan na Sansepolcro inda ya sami ilimin abbaco. Wannan shi ake Kira da ilimin yaren gari ( watau, harshen gida) maimakon yaren harshen Latin kuma sannan ya mai da hankali akan ilimin da ake buƙata na 'yan kasuwa. Sunan Mahaifinsa Bartolomeo Pacioli; duk da haka, an ce Luca Pacioli ya zauna tare da iyalin Befolci tun yana yaro a garin sa na haihuwa Sansepolcro. Ya yi hijira ya koma Venice a shekarar 1464, inda ya ci gaba da karatunsa yayin da kuma yake aikin karantarwa a matsayin malami dake karantar da 'ya'ya uku na wani dan kasuwa. A cikin wannan lokaci ne ya rubuta littafinsa na farko, wani littafi kan ilmin lissafi ga yaran da yake koyarwa. Tsakanin 1472 da 1475, ya zama ɗan fariar Franciscan . [3] Don haka, ana iya kiransa Fra ('Friar') Luca.
A cikin shekarar 1475, ya fara koyarwa a Perugia a matsayin malami mai zaman kansa kafin ya zama shugaba na farko a lissafi a 1477. A wannan lokacin, ya rubuta cikakken littafin karatu a cikin yaren gida domin ɗalibansa. Ya ci gaba da aiki a matsayin mai koyar da ilimin lissafi mai zaman kansa kuma an umurce shi da ya daina karantarwa a wannan lokacin a cikin garin Sansepolcro a cikin 1491. A cikin 1494, littafinsa na farko shine, Summa de arithmetica, geometria, Proportioni et proportionalita</link> , Wanda aka buga shi a garin Venice. A cikin 1497, ya karɓi sakon gayyata daga Duke Ludovico Sforza don yin aiki a Milan . A can ne ya had da, kuma ya koyar da ilimin lissafi, ya haɗa kai da kuma ya zauna tare da Leonardo da Vinci . A shekara ta 1499, Pacioli da Leonardo aka tilastawa barin Milan lokacin da Louis XII na Faransa ya kwace birnin kuma ya kori majiɓincinsu. Ya bayyana cewa a ƙarshe sun rabu a cikin shekarar 1506. Luca Pacioli ya mutu yana da shekaru 70 a ranar 19 ga watan Yuni 1517, wanda ake tunanin a garin Sansepolcro ne ya mutu inda anan ya kare yawancin rayuwarsa na ƙarshe.
Lissafi
[gyara sashe | gyara masomin]Pacioli ya buga tare da wallafa ayyuka sa da yawa akan ilimin lissafi, Wanda ya haɗa da.
- ↑ Benedetto Cotrugli predates him with the idea of a double-entry system with his manuscript Della Mercatura e del mercante perfetto which was written in 1458, but officially published in the 16th century.[Ana bukatan hujja]