Academia.edu no longer supports Internet Explorer.
To browse Academia.edu and the wider internet faster and more securely, please take a few seconds to upgrade your browser.
2022
Marubutan wannan Littafin sun tattara wasannin gargajiya na Hausawa guda ɗari biyu da goma shahuɗu (214) a shekara ta 2021. Sun wallafa su a cikin littafi mai suna Wasanni a Ƙasar Hausa. Littafin ya ƙunshi dukkannin nau’ukan wasanni – na kwaikwayo da waɗanda ba na kwaikwayo ba. Daga baya ne suka yi tunanin ware wasannin kwaikwayo daga cikinsu. An yi nasarar ware wasannin kwaikwayo guda 50. An raba littafin zuwa babuka shida (6). Babi na farko yana ɗauke da gabatarwa. A ciki an kawo bayani game da ma’anar wasan kwaikwayo. An kuma kawo amfanin wasannin kwaikwayo da rabe-rabensu. Babi na biyu zuwa na biyar kuwa na ƙunshe da bayanai game da wasannin kwaikwayo na gargajiya daban-daban. Sun haɗa da na yara maza da yara mata da na tarayya. A gefe guda kuwa, an kawo na manya maza da mata. Babi na shida wanda shi ne na ƙarshe, yana ƙunshe da bayani game da tasirin zamani a kan wasannin kwaikwayon Bahaushe na gargajiya.
Jalingo Journal of Linguistics and Literary Studies (JAJOLLS), 2021
Nau’o’in wasan kwaikwayon Hausa aikatacce da rubutacce ba su daɗe ba idan an kwatanta da rubutacciyar waƙa da rubutun zube. Cikin wannan bincike an bi diddigin tarihin samuwar aikatacce da rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa. Kamar yadda binciken ya gano an fara samun rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa tun daga ayyukan Haji Ahmadu Kano (1898) da Rudolf Prietze (1924) ta hanyar amfani da labarum gargajiya da hikiyoyi.Yayin da, a gefe guda, aikatcce kuwa ya fara bayyana a ƙarshen gomiyar shekarar 1930 cikin wasannin da Malam Aminu Kano (1938) ya shisshirya da kuma na Abubakar Tunau (1943) ta hanyar dandamalantar da ƙirƙirarrun wasannin kwaikwayo. Haka kuma wannan takarda ta kawo nau’o’in ruhin aikatacce/rubutaccen wasan kwaikwayo guda tara (9), sannan aka ƙarƙare bitar wannan bincike da hanyoyi guda bakwai (7) waɗanda akan bi wajen samar da wasannin kwaikwayon Hausa. Fitattun Kalmomi: wasan kwaikwayo, aikatacce, rubutacce, mashiryin wasa, marubucin wasa
IAR Consortium, 2021
Wannan bincike da aka yi wa suna “Laƙabi Linzamin Makaɗa da Mawaƙan Hausa” an gudanar da shi ne domin tabbatar da tasirin amfani da sunayen laƙabi ga Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Manufar binciken ita ce a nazarci sunayen rukuni daban-daban na Makaɗa da Mawaƙan Hausa domin a karkasa sunayensu na laƙabi ta yadda za a sami wakilcin rassan laƙubban Hausa bisa mizanin awon ayyukan da suka gabata. Haka kuma nazarin yana da manufar tabbatar da tasirin laƙabi ga al’ummar Hausawa musamman ga mutanen da suka yi fice a kan wasu harkoki na rayuwa kamar Makaɗa da Mawaƙa. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari su ne tattara bayanai musamman na sunayen Makaɗa da Mawaƙan Hausa waɗanda aka samu a ayyukan da aka yi a kansu a littattafan magabata. Haka kuma an yi amfani da waƙoƙin Hausa da dama waɗanda ke ɗauke da sunayen makaɗan. Misalan da aka kawo na sunayen makaɗan su ne makamashin nazarin. Wannan nazarin ya yi nasarar tabbatar da cewa, yawancin Makaɗa da Mawaƙan Hausa suna amfani da sunayen laƙabi ba kamar sauran jama’a ba da za a iya samun masu amsa sunan yanka kawai. Haka kuma nazarin ya yi nasarar gano cewa, sunayen laƙabin mawaƙan Hausa shi ya fito da su a fili. Jama’a sun fi riƙe da amfani da sunayen laƙabi na Shata da Ɗanƙwairo da Ɗandawo da Ɗan’anace da Narambaɗa fiye da sunayensu na yanka.
M.A. Dissertation , 2021
The internet has become an indispensable aspect of human life. Today, if the internet should cease to exist for just an hour, the magnitude of catastrophic consequential loss that will follow is unimaginable. Several academic fields and languages have wholeheartedly embraced the internet. Hausa is one of the developing languages on the internet. By the end of 2020, there were at least 44 highly visited Hausa websites with diversed contents and high online visibility. On this basis, research works should be conducted about the Hausa on the internet to ascertain the current situation and scenarios as well as to see to the improvement of same. The objectives of the research are to study the (i) Hausa culture-based internet contents, (ii) the attainments and challenges surrounding Hausa websites and blogs, and (iii) determining sustainable measures for enriching and dissemination of Hausa culture-based contents on the internet. The scope of the study is limited to Hausa culture within the domain of the internet. The study methodologically used interviews and online textual analysis in obtaining the research data. Platonism is adapted as a theory that guides the research, on the basis of which the research opines the existence of a physical world and an incorporeal world – the latter being the internet. It is also based on the Hausa philosophy that “zamani riga ce” (change before you have to), which emphasizes that the Hausas should embrace and utilize the internet as a precaution to being poorly represented. The research confirms that today, nothing can be successful and earn global recognition and acceptance without the help of the internet. It also realizes that, though the Hausa culture is spreading more on the internet, Hausa websites and blogs face a lot of challenges one of which is inadequate knowledge of the language by the websites and/or blogs administrators. Finally, the research offers some recommendations among which one is that the individuals and authorities concerned - including agencies, departments, instructors, and researchers - should make efforts to ensure adequate representation and presentation of Hausa on the internet.
Wannan aiki ya mayar da hankali ne kan tasirin biɗa (nema) da tanadi (tattali) ga cigaban tattalin arziƙin Bahaushe. Takardar ta yi bitar ma'anoni da kamanci da kuma wasu bambance-bambancen da ake iya samu tsakanin kalmomin guda biyu. Bayan haka, an nazarci yadda lamarin ya ke ga Bahaushen yau. Bugu da ƙari, an yi bitar gurbin biɗa da tanadi ga bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe. Domin binciken ya kuɓuta daga jin kunyar ilimi da masu ilimi, an bi manyan hanyoyi bincike guda biyu waɗanda da su ne aka yi amfani wajen tattara bayanai yayin binciken. Hanyoyin su ne, bitar ayyukan da suka gabata da kuma tambayoyi. An ɗora aikin kan tunanin Bahaushe na "Mai nema na tare da samu." Binciken ya gano cewa, biɗa da tanadi ba a matsayin tasiri kawai suka kasance ba, su ne ke tallafe da tattalin arzikin Bahaushe a tarihance. A ɓangare guda kuma, tasirin zamani da sauye-sauyen yanayi ya kawo sauyi ga yadda tsarin yake a baya. Hakan kuwa ya samar da giɓi bayyananne ga tattalin arziƙin Hausawa, duk kuwa da cigaban da aka samu a ɓangare guda. A bisa haka ne takardar ke ba da shawarar cewa, a yi hoɓɓasar nazartar hanyoyin ɗinke wannan ɓaraka a matakin ɗaiɗaikun al'umma da gundumomi da kuma a gwamnatance. 1.0 GABATARWA Duk da cewa akwai fasahohin rayuwa da ba su zo wa Bahaushe ba sai bayan cuɗanyarsa da baƙin al'ummu, 1 abin ba haka yake ba ga falsafar biɗa da tanadi. A wannan ɓangare, sai dai a ce: "Tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta!" A rayuwar Hausawa, biɗa da tanadi na da tsohon tarihi. Hasali ma, Hausawa sun shahara ta fuskar noma da kasuwanci da fatauci da sauran sana'o'i daban-daban. Ficen da Hausawan suka yi a ɓangaren sana'o'in fatauci da kasuwanci ya taimaka matuƙa wajen bazuwarsu zuwa wurare daban-daban. Hausawa sun kafu a ire-iren waɗannan wurare tare da cigaba da gudanar da sana'o'insu. 2 Wannan takarda ta dubi yadda lamarin biɗa da tanadi ya ke a Bahaushiyar rayuwa. An waiwaiyi yadda abin yake a da, tare da nazartar sauye-sauyen da aka samu. Kamar yadda Bahaushe ke cewa: "Zamani riga ne." Wanda bai saka rigar ba, haƙiƙa dole ya bayyana tsirara. Ke nan dai cigaban tattalin arziƙin Hausawa a yau ba zai samu ba sai Hausawan sun taka nau'in rawar kiɗan da zamani ke rangaɗawa. Duk kyawun tsarin salo na biɗa da tanadin Bahaushe na gargajiya, ba dole ne ya dace da zamani ba. Wannan kuwa duk da cewa, a ɓangare guda bin zamanin na kawo koma baya ta wasu fuskokin zamantakewa. Hakan ya fi shafar haɗin kai da zaman "ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda" wanda shi kansa ya kasance wani babban jigo ga bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe. 3 1.1 MANUFAR BINCIKE Maƙasudin wannan aiki shi ne bitar gurbin biɗa da tanadi ga bunƙasar tattalin arziƙin Hausawa. Kai tsaye aikin zai mayar da hankali a kan: a. Nazartar tasirin biɗa ga bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe. b. Nazartar tasirin tanadi ga bunƙasar tattalin arziƙin Bahaushe. c. Nazartar biɗa da tanadi a zamantakewar Hausawa a yau. 1 Sani da Umar, (2008: 19) sun rawaito Yahaya, (1988) da Musa, (2013) da kuma ALS, (2015), duk sun nuna cewa, ana rubutun Ajami ne ta hanyar amfani da harrufan Larabci. Rubutun boko kuwa, ana amfani da harrufan Romanci ne. A taqaice, an sami waxannan nau'o'in rubutu bayan cuxanyar Hausawa da baqin Larabawa da kuma Turawa. 2 Sabo Ibadan babban misali ne na mazaunin Hausawa da ya kasance ba a qasar Hausa ba. 3 A tarihance, al'adun da suka shafi kara da taimakon juna na "mu gudu tare mu tsira tare" na matuqar taimaka wa tattalin arzikin Hausawa. Al'adun da suka shafi xaure da xauke da aro da gudummuwa (da makamantansu) sun daxe suna tallafa wa tattalin arzikin Hausawa. Ta hanyarsu ne ake rufa wa juna asiri.
Zamfara International Journal of Humanities, 2023
Manufar wannan maƙala ita ce nazartar al’adun Hausawa a duniyar intanet ta yau. An ɗora aikin kan Bahaushen ra’i na Zamani Riga. Kadadar binciken ta taƙaita ga al’adun Hausawa da duniyar intanet. Tushen bayanai na farko da aka yi amfani da su sun kasance kafafen intaent kai tsaye. Majiya ta biyu kuwa ta kasance ayyukan da suka gabata da ke da alaƙa da wannan bincike. Sakamakon binciken ya nuna cewa, tuni Hausa ta kama hanyar samun gagarumin gindin zama a duniyar intanet. Al’adun Hausawa daban-daban na bayyana yayin da aka neme su ta hanyar injunan nema na kan intanet. Ƙalubale da ake fuskanta a wannan haujin sun haɗa da ƙarancin masana da ke jagorancin lamuran kafafen intanet na Hausa, da kuma rashin ingancin bayanai. Daga ƙarshe binciken ya nuna tilascin ƙara himma ga masana da manazarta harshe da al’adun Hausawa wajen sanya rigar zamani da samar da kyakkyawan wakilci a duniyar intanet.
An dad’e ana amfani da wasannin kwaikwayo wajen isar da sak’wanni ga al’ummar Hausawa. Sak’wannin sun shafi ilimantarwa da fad’akarwa da nishad’antarwa. Kuma suna yin tasiri a cikin rayuwar al’umma. Wasannin da ake shiryawa ba su tsaya kan jigogin da aka gina su sun daidaita ba. Hakan na faruwa ne sakamakon kwaikwayon al’adun wasu al’umomi da suka had’a da Turawa, da Indiyawa da sauransu. Hakan ta kai ga wasu manazarta na kallon cewa, batun maganar fina-finan Hausa suna wakiltar al’adun Hausawa sai dai a kitse da k’wark’wa kawai. Lokuta da dama ma ana ganin cewa, idan aka cire harshen da ake amfani da shi cikin fina-finan (Hausa), to ba su da wata sauran alak’a da al’adun Hausawa. Wannan ya sa abin ya zama bambarak’wai nono da gishiri. Wannan takarda ta tarkato wasu daga cikin d’abi’u kamar yadda suke fitowa a cikin wad’annan fina-finai na Hausa. D’abi’un sun had’a da sutura da magana har ma da halayya. Hakan ya haifar da samuwar wasu miyagun d’abi’u tattare da rayuwar al’ummar Hausawa ta yau da kullum.
2021
Wannan maqala ta kunshi bayanai kan Rayuwan mutane game da giya, ca-ca da lodo kafin zuwan Musulunci, abubuwa biyar da musulunci yazo don tsaresu wa dan-Adam, menene ma’anar giya a musulunci ko kwaya?, dalilen da yasa mata/maza ke shaye-shaye, bayanin kan miyagun kwayoyi, matakan sharia game da hana giya da kwayoyi a musulunci, hukuncin wanda ya sha giya ko kwaya a musulunci, nauoin kwayoyi da tasirinsu ga dan Adam, illolin shaya-shaye ga mace ko namiji a musulunci, Mafita game da shaye-shaye.
Слово і час, 2023
(Terni, 7 giugno 2024) - Camera Civile di Terni, 2024
International Journal for Research in Applied Science & Engineering Technology (IJRASET), 2022
Asian Journal of Criminology, 2009
Science (New York, N.Y.), 2017
Zoological Journal of the Linnean Society, 2015
The Asia-Pacific Journal: Japan Focus, 2007
Revue Belge d'Histoire Contemporaine, 2024
Journal of Biomedical Materials Research, 2003
Forestry and Forest Melioration