Location via proxy:   [ UP ]  
[Report a bug]   [Manage cookies]                

Uwanta

Download as doc, pdf, or txt
Download as doc, pdf, or txt
You are on page 1of 29

.

MATSAYIN AURE
DA HAKKIN

MA'AURATA
Muhammad inuwa hassan
Gombe gombe state

. Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya Aure
hanya ce na kamewa da kuma tsare kai Allah ya
umarci musulmai wajen sauka-ke hanyarsa
dakuma sanadinsa. Allah yayi alkawari ga
wadanda suke bukatar Aure cikin tsare musu
kawunansu gameda afkawa haram, domin xai
wadatar dasu ya kuma buda musu/ko yalwata
musu a cikin arzikinsu. Kamar yadda madaukakin
sarki yake cewa: "kuma ku aurar da ya’yan ku
ok gareku, da salihai daga bayinku, da
kuyangunku, idan sun kasance matalauta, Allah
zai wadatar dasu daga fala-larsa, kuma Allah
mawadacine, masani".
Tsirada aminci su tabbata ga fiyayyen halitta
maicikakken halitta dakuma cikakken hankali,
aikoshi rahamane gatalikai bakidaya,
shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa
gamida sahabban sa harzuwa ranartashin
alqiyama Allah yasa damu acikinsu.

‫ حقيقة فى الوطاء مجاز فى العقد‬:‫النكاح لغة‬ .


‫ أى حقيقة فى العقد مجاز فى الوطاء‬،‫ففى العسكى‬:‫وأماالصطالحا‬
Ma'ana

Aure:
Kalmar Aure a harshen larabci "shine haduwa
ko kuma saduwa" mujaxinsa kuma "shine
kullawa" Amma a shari'ance "shine kulla Aure
Tsakanin namiji da mace wanda zai halatta
saduwa a tsakaninsu".

Kalmar Aure a harshen larabci itace an-


nikahu. Ita kuwa wannan kalmar tanada ma'ana
biyu :Ma'anarta ta harshe da Ma'anarta ta shari'ah.
Ma'anarta ta harshe itace haduwar wani Abu da
wani Abu, wato idan Aka hada Abu biyu sai ace
anyi musu Aure, ko sunyi Aure.

Amma Ma'anar Aure ta shari'ah, itace daura


Aure Tsakanin mace da namiji, ta yadda zai
halatta garesu, su kadaita da juna su biya bukatar
jindadi na mutuntaka a tsakaninsu, ta hanyar da
shari'ah ta tsara musu.
‫حكمه‬ :
‫شرع‬
‫ وانفسه أهمها ما يلى‬،‫ ودينه‬،‫ وقيم اجمتماعية‬،‫شرع النكاح فى اإلسالم لتحقيق معان‬

‫ هللا من أربعة أوجه‬1‫ و فى ذالك قرية إلى‬،‫حفظ النوع اإلنسانى بااإلستكثار من النسل‬ .

Hikimar yin Aure

An shari'anta yin Aure a cikin musulunci


domin tabbatar da Ma'anar Aure da kuma
tsayuwan zamantakewa da addini da rai mafi
muhimmancinsa gashi kamar haka.

1. Tsare nauyin Dan Adam wajen yawaita da


samun 'ya'ya, a cikin wannan akwai kusantuwa
zuwa ga Allah gameda Abu-buwa guda hadu.

a). Dacewa da soyayyar Allah wajen yin aiki


gameda samun da, domin wanzuwan jinsin Dan
Adam a bayan duniya.

b). Neman yardan manzon Allah (S. A. W) cikin


yawaitar wadanda manzon Allah zanyi alfahari
dasu, kamar fadinsa (S. A. W) "ku auri masu
haihuwa masoyanku, domin ni zanyi alfahari da
yawanku ga sauran Annabawa ranar tashin
alqiyama.

c). Neman tabarraki gameda yaron na kwarai


bayan rasuwan mahaifinshi saboda fadin manzon
Allah (S.A.W) "idan Dan Adam yarasu duk
ayyukansa sunyanke sai dai abubuwa guda uku
(3):

i. Sadaqa mai gudana (shine kamar mutum yagina


masallaci, ko makaranta, ko tona rijiya/bohol, ko
yadasa bishiya) to bayan rasuwan sa duk wanda
yayi amfani da wannan yana da lada.

ii. Ko mutum yanemi ilimi kuma ya ilmantar.

iii. Ko yaro nakwarai wanda zai masa addu'a


bayansa. (imamu muslim ne ya rawaito).
d). Neman ceto gameda rasuwan Dan mutum
karami daya rasu kafin shi.

Hikimar yin Aure

a. Shiya banbanta rayuwar Dan Adam data dabba:


Ubangiji ya fifita Dan Adam Akan sauran halittu.
Ya bashi damar sarrafasu don amfanin kansa. Ya
kuma kyatata halittarsa. Yabashi hankali, wanda
da shine yafi dabbobi, ya kuma bashi damar yin
amfani da hankalinsa da kwakwalwarsa wajen
ilmantuwa. Allah ya baiwa Dan Adam wadannan
darajoji ne domin ya kaddara yaxama halifansa a
bayan kasa.
To kuwa, idan Allah ya baiwa Dan Adam
wadannan darajoji ne domin ya zama halifansa a
bayan kasa, babu shakka ya kamata, ko kuma ya
wajaba, rayuwarsa tazama ta banbanta da sauran
dabbobi. Domin haka, atakaice, babbar hikimar
yin Aure itace domin rayuwar Dan Adam ta
banbanta da ta dabbobi. Allah ya umarci mutum
daya biya sha'awarsa ta hanyar Aure, domin
asamu dangantaka a Tsakanin Dan Adam. Wato a
samu yaro da uba, da uwa da yayye da kanne. A
samu jikoki da kakanni, da surukai da sauran su.
Babu shakka baza'a sami irin wadannan
dangantaka ba idan Aka bar Dan Adam yayi
saduwa irin dabbobi. Wato ta hanyar zina. Ta
hanyar saduwar Aure ne mutum zai fahimci
danginsa, da kabilarshi da al-ummarshi, wadanda
su sukan taimakeshi yayin da wani abin farin ciki
ko bakin ciki ya sameshi. Wannan shine abin da
ubangiji ya bayyana mana a littafisa mai tsarki
inda yake cewa:

‫يأيها الناس إنا خلقنكم من ذكر وأنثى وجعلناكم شعوبا وقبآئل لتعارفوا إن أكرمكم عندهللا أتقكم' إن هللا عليم خبير‬ "

"yaku mutane! Mu mun halicceku daga mace da


namiji, kuma mun sanyaku dangi kuma kabila-
kabila, domin kusan junanku. Wanda yafi girma
cikinku a wajen Allah shine yafi tsoron Allah.

b. Shine hanyar kaucewa zina da illolinta:wato


hikimar yin Aure itace, yinsa dabin ka'idojinsa a
musulunce yana rage yaduwar zina da yaduwar
illolinta a tsakanin al-umma. Ya kamata mu
bayyana kadan daga cikin illolinta, domin mu
dada fahimtar hikimar dake cikin wannan tsari
wanda shari'ah tayi umarni dashi.

1- ita zina dabi'ace wadda take mayarda Dan


Adam yarikayin rayuwa ta dabbobi ;koma ta gaza
ta dabbobi. Domin xai zama babu banbanci
tsakaninsa da jaki ko doki ko akuya, yayin da
yaso biyan bukatar.

2. Yaduwar zina tana jefa mata cikin wulakanci


da halin kaka nikayi. Wata mujalla ta amurka
wadda ake kira "time Magazine" tataba bayar da
bayanin irin yadda zina ta yadu a amurka.
Wannan mujallu tanuna Cewa a kowanne minti
(7), sai anyi fyade a kasar wato sai ansamu wani
namiji da ya fadawa mace da karfin tsiya yayi
lalata da ita. Mujallar takara cewa, babu wata
hanya wacce mace zata kwaci kanta sai dai suyi
amai ko fitsari koma bayan gari".
Abun takaici shine, bayan yan shekaru kadan da
faruwar wannan a amurka, sai gashi a nigeria,
kuma ta arewa anasamun mutum ya dauke
amarya. Mace bata isa ta fita ba, sai su dauketa da
karfi suje su boyeba harsai Lokachin da suka
Gama lalata da'ita, Sannan idan sunga dama
susaketa, ina wulakancin dayafi wannan ga 'ya
mace?

3. Tana farar da kiyayya Tsakanin Jama'a. Domin


duk mutumin da ya sami labarin wani yana
neman matarsa ko 'yarsa ko kanwarsa, ko
mahaifiyar sa da zina, gaba zatashiga Tsakaninsu,
idan ma bainemi halakashiba.

Ance wata rana wani mutum ya ta6a zuwa ya


tambayi Annabi Muhammad (SAW) izinin yin
zina. Sahabbai sukayi masa tsawa, sai Annabi
(SAW) ya dakatar dasu, sai yatambayeshi,
koyanason wani yayi zinar da 'yarsa ko kanwarta
ko mahaifiyar sa ko matarsa? Mutuminnan
yanuna bayaso. Sai Annabi Muhammad (SAW)
ya nuna masa cewa, duk wanda zai yi da'ita Lallai
ne tazama 'yar wani, ko mahaifiyar wani, ko
kanwar wani, ko matar wani, su kuma bazasu
soba. Anan ne wannan mutumin yashiga tunani.
Ya gano illar zina Kam farar. A nanne akace
Annabi Muhammad (SAW) yadafa kirjinsa yace:

‫اللهم امرقلبه وسدد لسانه‬

Ma'ana

Ya ubangiji kashiryadda zuciyarsa, ka daidata


harshen sa, Allahu akbar! Ance tun daganan
mutumin baisake jin sha'awarsa tayin zina ba.

4. Tana wargaza tsarin nasaba da dangantaka.


Domin ita zina tana yaduwa ne tsarin auratayya
yana yin rauni. Daga nan sai kokonto yafara shiga
zukatan iyaye da 'ya'yaye. Uba yafara kokonto ko
dansane ko ba dansabane. Da ya shiga tunani.
Gameda mahaifinsa. Idan kuwa haka ta faru,
shegu zasu yawaita. A duk kasar da shegu suka
yawaita kuwa, sukan zama gagarumar matsala ga
hukuma da mutanen kasa baki daya. Domin zasu
rika kai farmaki ga rayuwar Jama'a.

5. Yaduwar zina yakan sa yaduwar cututtuka a


Tsakanin al-umma. Ada dai cutar ciwon sanyi
akasani zina tana yaduwa. A karshen wannan
karni na ashirin (2000), saiga wata cuta da ake
kira "AIDS" wanda take lalata garkuwar jiki
wannan cuta ta ruda duniya gaba daya a wannan
karni. Domin ankasa gano hakikanin maganinta.
Idan takama mutum saita kaishi kabari. Shine ma
ya sa ake kiranta (KABARI SALAMU
ALAIKUM). Ance wannan cuta ta fitone daga
amurka, daga wajen mazinata da yan luwadi.

6. Zina tana kawo gurbacewar zaman tare


tsakanin mutum da iyalinsa. Idan mace tafahimci
mijinta mazinacine, ko miji yafahimci matarsa
haka take, ba a samun samun amincewa da juna a
tsakaninsu, ko da zaman ya yiyu akan yishi ba
cikin dadi da kwanciyar hankali ba.

Zina tana jawo tabarbarewar tattalin arziki na


gida da lalacewar biyayyar yara. Yabada waya
magidancin da yake wannan mummunar dabi'a a
tarar yana wadata kida wajen abinci ko sutura.

Muhimmancin yin Aure a shari'ar musulunci

Allah (SAW) ya ja hankalinmu ga Aure inda yake


cewa:

‫ إن فى ذالك أليت لقوم يتفكرون‬،‫ومن ءايته أن خلق لكم من أنفسكم أزواجا لتسكنوا إليها وجعل بينكم مودة ورحهة‬

Ma'ana

"Daga cikin ayoyin sane ya halicci mataye a


gareku daga kawunanku, domin ku natsu a
garesu, ya sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu
ku, hakika da a kwai alamom na ganin Girman
Allah a cikin wannan, ga mutane masu tunani.
Suratu rum: Aya ta (21)

Bukhari da muslim sun rawaito daga Abdullahi


bn Mas'ud cewa manzo Allah (SAW) yace:

‫ فإنه له وجاء‬،‫ ومن لم يستطع فعليه بالصوم‬،‫يامعشر الشباب من إستطاع منكم الباءة فليتزوج فإنه أغض للبصر وأحصن للفرج‬ ."

Ma'ana

"yaku taron samari, wanda yasamu iko daga


cikinku to yayi Aure, shine yafi taimako wajen
hana kalle-kalle (kallon mata) kuma yafi
taimakawa wajen kiyaye farji, wanda bai samu
ikoba to yayi azumi, domin shi garkuwane a
gareshi".

Abdullahi bn Mas'ud yakasance yana cewa:


"Koda za'ace kwana gomane kawai ya rage a
rayuwata sai naso yin Aure", domin kada nasadu
da ubangiji ina gwauro". Shikuwa mua'zu bn
jabal cewa akayi matansa biyu sunrasu a dalilin
annoba, yayin da shima din yake kan hanyar sa ta
mutuwa a wannan annoba. Amma sai yace
"kiyimin Aure, domin ina gudun insadu da Allah
gwauro / duba ihya'u ulumassini, juzu'i na biyu 2
shafina 12.

Haka kuma ance ahmad bn hambali yayi Aure a


rana ta biyu bayan rasuwar uwar dansa Abdullahi
yana cewa: " banason nakwana ina gwauro".

Ihya'u ulumuddin, juzu'i na 2 shafi na 13

‫حكمه‬ ))
‫ كما هوواضح من مجموع أقوالهم‬.‫لذانجدالفقهاء يقسمون النكاح إلى األقسام التالية‬ .

Hukuncin yin Aure a shari'an musulunci

Saboda haka muka samu malamai masana fiqhun


musulunci suna raba Aure zuwa ga rabuwa kamar
haka:

1.:‫النكاح الواجب‬

‫ وهو اقول عامة الفقهاء‬،‫ ويخشى على نفسه الزنا إن لم ينكح‬،‫ وهو يملك مئونته‬،‫يكون النكاح واجب فى حق من تتوق نفسه إليه‬ .

Wajibin Aure

Aure yana kasan cewa Wajibi Akan mutum daga


wanda ya mallaki abun da zanyi Aure. Ma'ana
yanada halin da zai iya ciyarda matar da tufatar
da ita dasamar mata da wajen zama kuma yana
tsoro idan baiyiba zanyi zina to wannan shine
fatawa mafiya yawa daga cikin malamai na
musulunci.

1. ‫ النكاح‬:‫المقدمة‬

‫ ويأمن على نفسه من الموقوع فى الحرام‬،‫يكون النكاح سنة فى حق من يملك القدرة عليه و على مؤونته‬ .
‫ وهو بالنسبة له أولى من نركه حتى ولو كان للتفرع للعبادة فى قول جمهورالفقهاء؟‬،‫فهذا يستحب له النكاح‬
Mustahabbi ko mandubi

Aure yana kasancewa sunnah ga wanda yake da


ikon yin Auren kuma zai iya daukar dawainiyar
Auren Amma kuma shiya aminta wa kansa shi
bazaiyi zinaba.

Aure yana zama Mustahabbi Akan mutum idan


zai iya danne sha'awarsa batare da yayi zinaba
kuma yazamto zai iya yin Auren yarike matar
Tareda biya mata sha'awarta ko kuma yakasance
Sha'awa bata dameshiba Amma yanason haihuwa
kuma zai iya biya bukatar matar don musulunci
bai goyi bayan zama babu Aure ba ko da maiyin
ibadane haka Annabi Muhammad (SAW) yana
son al ummar sa suyi Aure su haihu domin fatan
yaran zasu samu Tarbiyya su zama musulmai na
gari.
3. ‫ النكاح‬: ‫المكروه‬
‫ أو فتور الرغبة عنده‬،‫ لعجنره عن اإلنفاق‬،‫بكون النكاح مكروها فى حق من يخشى على نفسه الوقوع فى الضرر لزوجه إن نكح‬
‫ا‬

Makruhi

Aure yana zama makruhi ga wanda yake ganin


zai iya cutar da matar in yayi Auren saboda bazai
iya ciyar da ita ba kuma bai da yawan Sha'awa ga
mata ko ya zamanto ita zata dau nauyi kanta rabi
da rabi.

: 4. ‫المحرم النكاح‬

‫ فيكون‬،‫ ألن مايؤءى إلى الحرام يكون حراما‬،‫ أوكان يعلم من نفسه الظلم إن نزوج‬،‫يكون النكاح حراما فى حق من ال يملك مؤنته‬

‫حراما لغيره‬ .

Aure yana zama haram Akan mutumin da bai


mallaki abunda zanyi Aure ba ko kuma idan ya
auri matar ma zaluntar ta zaiyi to abunda zai
kaika ga aikata haram to shima kansa haram ne a
wurin mutum.

Kuma ya zama shi baya jin Sha'awa ma'ana


Sha'awar mata bata dameshiba.

: 5. ‫الحالل النكاح‬

Halal

Aure yana zama halal idan mutum ba shida


Sha'awa baya bukatar haihuwa Amma zai biyawa
matar bukatar ta.

‫الحقوق الزوجية‬

‫ " ولهن مثل الذى عليهن‬-:‫يجب للزوجة على زوجها حقوق كثيرة تثبت لها بقول هللا تعالى‬:‫ حقوق الزوجة على زوجها‬-‫أ‬

228)‫ (البقر‬.‫بالمعروف‬ )"

‫" إن لكم من نشائكم حقا‬:‫ويقول الرسول صلى هللا عليه وسلم‬


"
‫ولسنانكم عليكم حقا‬

‫ومن هذه الحقوق‬ :


* ‫ "نطعمها‬:‫نفتها من طعام والشراب وكسوة وسكنى بالمعروف لقوله صلى هللا عليه وسلم دم لمن سأله عن حقالمرأة على الزوج‬
‫ والتضرب الوجه والتهجر اال فى البيت‬، ‫وتكسوها إذا كتسيت‬، ‫إذ طعمت‬ .
*

Hakkokin Ma'aurata

A- Hakkin mata Akan mijinta suna da yawa


tabbatacce ne cikin Al-Qur'ani da hadisi kamar
yadda Allah madaukakin sarki yake cewa "kuma
su matan suna da kamar Abinda yake akansu
yadda aka sani" manzon Allah (S.A.W) yana
cewa "Tabbas matanku suna da hakki Akan ku
kaman yadda kuma kuka da hakki Akan su ya
daga wadannan hakkoki.

1- Ciyar da ita, shine ne mutum ya ciyar da abinci


da shayar da ita da yi mata tufafi da nema mata
wajen zama tare da kyautatawa saboda fadin
manzon Allah (S.A.W) lokacin da aka tambaye
shi hakkin mata akan mijinta sai manzon Allah
(S.A.W) yace "kaci da ita idan kaima kaci ka
tufatar da ita idan kaima ka tufatar, kuma karka
mari fuskar ta karka munana ta,ma'ana kace Allah
ya wulakanta fuskar ki Sannan karka kaurace
mata sai acikin daki ma'ana karka fita a cikin
dakin ta ka koma wani dakin.

2- Ya jiyar da ita dadi, ma'ana wajibi ne akan


mijin yayi jima'i da ita Koda sau daya ne a cikin
wata hudu har in ya kai bazai iya yin jima'i da ita
ba kenan saboda fadin manzon Allah madaukakin
sarki "ga wadanda suke yin ranstuwa daga matan
su akwai jinkirin wata hudu,to idan sun koma to
Lallai ne Allah mai Gafara ne mai jin kai".
Bankara, aya 26.

3- Ya kwana tare da ita cikin wani kwana hudu ya


kwana a wajen ta domin haka aka hukunta a
zamanin sayyidina Umar Allah ya kara masa
yarda, ma'ana kada mutum ya wuce kwana hudu
bai zo ya kwana a dakin matarsa ba sai inda wata
lalura ta tafiya.

4- A raba musu komai da adalci:


Idan mutum ya kasance yana mata samu da yada
su biyu ne ko su uku ko hudu to yayi adalci cikin
duk abinda zai raba musu kada ya fifita wata akan
wata domin rashin yin adalci yana kowa
rushewan gida ya iya sa mata su taso suna gaba
da junan su saboda rashin adalci mai, Manzon
Allah (S.A.W) yana cewa "wanda ya kasance
yana da mata biyu karkata zuwa ga daya yana
birin daya zaizo ranar tashin al-kiyama gefensa
daya ya shanye yana jan gefe daya ne saboda ya
karnace". Allah ka tsaremu da rashin yin adalci ga
iyalammu Amin.

5- ya kwana a dakin amarya ranar da yayi Aure.


Idan mutum ya auri budurwa zaiyi kwana bakwai
a dakin ta bazawara kuma zaiyi kwana uku kamar
yadda manzon Allah (SAW) ya fada "budurwa
kwana bakwai, bazawara kwana uku Sannan
yadawo zuwa matansa.

6- Anason yabata dama domin ta gaida mara


lafiya wanda yake daga cikin muharramanta idan
bashida lafiya, hakanan yabata dama tayi gaisuwa
idan an yamasa hakkin tane yabata izini taje
xiyara daya daga cikin 'yan uwanta, kamar iyayen
ta da sauran sunmin. Matukar yin hakan bazai kai
da samun matsalaba.

‫حقوق الزوج‬

‫وللزوج على زوجته حقوق‬

‫ ولهن مثل الذى عليهن بالمعروف‬: ‫ثانية بقول هللا تعالى‬ .

‫ إن لكم من نسائكم حا" وهذه الحقوق هى‬: ‫ ولقوله صلى هللا عليه وسلم‬،‫فما عليهن هوحقوق الزوج‬

Ma'ana

Hakkokin miji Akan matarsa

Shi miji yanada hakkoki Akan matarsa kamar


yadda yazo tabbatacce a cikin Al'qurani mai
girma da fadinsa madaukakin sarki "kuma su
matan sunada kamar abun da yake Akan su yadda
aka sani. Kuma maza suna da wani daraja akansu
(mata). Abunda yake kan mataye shine hakkin
magajin su. Saboda fadin manzon Allah (SAW)
"Lallai kunada hakki Akan matan ku" wadannan
hakkoki gasu kamar haka:

‫ فتطيعه فى غير معصية هللا وبالمعروف‬: ‫الطاعة فى المعروف‬ *


‫ فإن أطعنلكم فال تتبعوا‬:‫فال ال تقدر عليه أو يشق عليها لقوله تعالى‬
‫عليهن سبيله‬

‫وسلم عليه هللا صلى الرسول وقول‬

‫لو كنت آمر احدا أن يسجد ألمرأة أن تسجد لزوجها‬ "

Ma'ana

1- tayimishi biyayya cikin abunda sha'riah ta


yarda dashi, zata yi wa mijinta biyayya matukar
bai sa6awa Allah da manzon saba, tayishi da
kyautatawa, bazatayiwa mijinta da'a ba cikin
abunda batada iko akai, ko abunda bazai yiwu ba
saboda fadinsa madaukakin sarki "sa'annan kuma
idan sunyi muku da'a to kada kunaimi wata hanya
akansu" da kuma fadin manzon Allah (SAW)
"dana kasance zan umarci wani ya sunkuyawa
wani, dana umarci mace ta sunkuyawa mijinta"
Ma'ana durkuso Abaiwa miji Abu ko agaisheshi,
to ba hakkin sa bane, hakkin Allah ne.

):‫ "فإن أطعنلكم فال تتبعوا عليهن سبيال(النساء‬: ‫وذالك قوله تعالى‬،‫حفظ ماله وصون عرضه وأن ال تخرج من بيته إالبإذنه‬
‫ وإذا أمرتها أطاعتك وإذا غبت عنها حفظتها فى‬،‫ خير النساء التى إذا نظرت إليها أسرتك‬: ‫وقول الرسول هللا صلى هللا عليه وسلم‬

)‫نفسها ومالك(ابو داوود‬.

Ma'ana

2- tatsare masa dukiyar shi da mutuncinshi,


kartafita daga gidanshi saida izinin shi, Saboda
fadin Allah madaukakin sarki "To salihan mata
masu da'ane, masu tsarewa ga gaibi saboda
abunda Allah yatsare" da kuma fadin manzon
Allah (SAW) "mafi alkairi mata, itace idan
kakalleta sai tasaka farin ciki, idan ka umarceta
kuma sai tayimaka da'a, idan bakanan a wajenta
kuma saita tsare maka kanta da dukiyarka, (Abu
dauda yarawaito).

‫السفر معه إذا شاء ذالك ولم تكن قد اشترطت‬

‫ إذا سفرها معه من طاعة الواجبة عليها‬، ‫عليه فى عقدها عدم السفر بها‬ .

Ma'ana

3- Tayi tafiya Tareda shi idan yaso hakan,


matukar dai ita batayi wani sharadi dashi ba
Lokachin Auren suba, cewa bazata bishiba idan
zaiyi tafiya, domin yin tafiya dareda mijinta da'a
ce kuma wajiba akanta.

‫ إذا دعاالرجل إمرأته إلى‬: ‫ لقوله صلى هللا عليه وسلم‬،‫ من حقوقه عليها‬،‫ إذا االستمتاعها‬، ‫تسليم تفسها له متى طلبها لالستمتاع بها‬

)‫ لعنتها المالئكة حتى تصبح" (متفق عليه‬،‫فراشة فأبت أن تجئ قبات غضبان عليها‬ .
4- Tasallama / mika kanta gareshi duk Lokachin
Daya nemeta domin biyan bukatar sa, domin
jindadi da ita yana daga cikin hakkokinshi akanta;
saboda fadin manzon Allah (SAW) idan
mutum/miji yakira matar shi xuwa ga shinfidarsa
sai taki yarda tazo, zata kwana da fushi akanta,
mala'iku zasu ta tsine mata harsai ta wayi gari.
(bukari da muslim suka rawaito).
‫ ال يحل للمرأة أن تصوم وزوجها‬: ‫استئذانه فى الصوم إذا كان حاضرا غير مساقر لقوله صلى هللا عليه وسلم‬
)‫شاهدإال بإذنه(متفق عليه‬

Ma'ana

5- neman izini miji idan xatayi azumi: idan


mijinta ya kasance y gare bayyi tafiya ba, to bai
halatta tayi azumin nafila ba sai ta nemi izinin sa.
Saboda fadin manzon Allah (SAW) : "baya
halatta ga mace da tayi azumi matukar mijinta
yana gari, (Ma'ana yana tare da ita a gidan) face
sai da izinin sa". (bukari da muslim suka
rawaito).

MUHADU A CIKIN LITTAFI NA GABA,


KASHI NA

KAMMALAWA
Godiya ta tabbata ga Allah mafi tsarkin suna,
salati da sallamawa da aminci ga mafi kyaun suna
shugaban halitta Muhammad Dan Abdullah sha
yabo, da iyalansa da alayensa gamida sahabban sa
har zuwa ranar tashin alqiyama Allah yasa damu
acikinsu,

Allah yasa wannan littafi ya amfanemu


arayuwarmu bakidaya kasanya albarka agaremu,
iyayen mu da suka mana Tarbiyya harmukakai ga
wannan lokaci Allah yakara musu lfy da albarka
wadanda suka rasu kuma Allah ya musu gafara da
rahama yasa aljannace makomarsu damu
bakidaya, Aamien ya Allah.

You might also like