Karas
Karas | |
---|---|
root vegetable (en) , food ingredient (en) da taproot (en) | |
Tarihi | |
Mai tsarawa | Daucus carota subsp. sativus (en) |
Karas yana daga cikin tsirrai watau kayan da ake nomawa watau kayan lambu, kayan marmari kuma, kalarsa ja ce, amma ba ja sosai ba, sai dai an fi noma shi a noman rani. Karas na da amfani sosai, domin kuwa yana magunguna daban-daban. Ga wasu daga magungunan da karas ke yi: Maganin bugun zuciya, taimakawa Ido, cututtukan baki da haƙora, ƙarfafa ƙashi, da dai sauransu. [1]
Yadda ake noman Karas
[gyara sashe | gyara masomin]• Da farko dai ana yin kaftu, bayan an yi kaftu sai a yi kwami, bayan an yi kwami sai ban ruwa. Daga nan sai a shuka ta bayan kwana biyar da shuka ta zata fito (tsiro). Daga nan sai a yi ta ban ruwa, bayan wani ɗan lokaci kaɗan sai a zo a yi cira (za a cire ciyarwa dake cikin ta) daga nan kuma sai a sa mata taki. Shi karas aƙalla ba ta wuce wata uku (3) da shuka sai kuma ta yi, a fara ɗiban ta. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ibrahim, Aminu (25 January 2020). "Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam". legit hausa. Retrieved 4 July 2021.
- ↑ Babanƙarfi, Aliyu (13 January 2020). "Noman rani a rafin Kubanni a gonar karas". Aminiya dailytrust. Retrieved 4 July 2021.